Hukumar tara kudaden haraji ta Nijeriya, ta ce ta hada gwiwa da kungiyar ‘yan kasuwa domin karbar harajin kayayyaki na VAT, daga miliyoyin kananan ‘yan kasuwa, a wani bangare na yunkurin fadada kudaden shiga da gwamnatin shugaba Tinubu ke yi.
Nijeriya dai ta na daya daga cikin kasashe mafi karancin tattara kudaden haraji a duniya da kusan kashi 10 cikin 100 na karfin tattalin arziki kamar yadda hukumar ta bayyana.
Kashi 47 cikin 100 kacal na kasafin kudin bana dai zai fito ne daga kudaden shiga sauran kuma daga rance.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hukumar ta ce ta na hada hannu da kungiyar ‘yan kasuwar Nijeriya, domin karba da kuma fitar da kudin harajin VAT daga ‘ya’yan ta, musamman wadanda ba na yau da kullun ba ta hanyar amfani da na’urar zamani.
Ta ce hadin gwiwar zai taimaka wajen dakatar da ayyukan masu karbar haraji ba bisa ka’ida ba a kasuwannin Nijeriya.