Home Labarai Ziyarar Aiki: Shugaban Jamus Ya Iso Najeriya

Ziyarar Aiki: Shugaban Jamus Ya Iso Najeriya

149
0
Frank Walter Steinmeier 20
Frank Walter Steinmeier 20

Shugaban ƙasar Jamus, Frank-Walter Steinmeier na ziyarar aiki a Najeriya.

Mista Steinmeier ya iso Najeriya ne a ranar Talata da daddare, inda ya samu tarbar ministan Abuja, Nyesom Wike bayan saukar sa a filin jirgin sama na Abuja.

A ziyarar da ake sa ran ta kwana uku ce, Shugaban na Jamus zai gana da Shugaba Bola Tinubu na Najeriya da kuma shugaban hukumar Ecowas, Alieu Omar Touray a nan Abuja.

Daga nan Mista Steinmeier zai wuce birnin Legas inda zai gana da wakilan kasuwanci da jami’an ƙungiyoyin fararen hula da na al’adu, ciki har da Farfesa Wole Soyinka.

Leave a Reply