Shugaban ƙasar Jamus, Frank-Walter Steinmeier na ziyarar aiki a Najeriya.
Mista Steinmeier ya iso Najeriya ne a ranar Talata da daddare, inda ya samu tarbar ministan Abuja, Nyesom Wike bayan saukar sa a filin jirgin sama na Abuja.
A ziyarar da ake sa ran ta kwana uku ce, Shugaban na Jamus zai gana da Shugaba Bola Tinubu na Najeriya da kuma shugaban hukumar Ecowas, Alieu Omar Touray a nan Abuja.
Daga nan Mista Steinmeier zai wuce birnin Legas inda zai gana da wakilan kasuwanci da jami’an ƙungiyoyin fararen hula da na al’adu, ciki har da Farfesa Wole Soyinka.














































