Home Labaru Ziyarar Aiki: Buhari Ya Dawo Najeriya Daga Kasar Chadi

Ziyarar Aiki: Buhari Ya Dawo Najeriya Daga Kasar Chadi

461
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo Abuja daga N’Djamena, kasar Chadi, inda ya halarci taron gangamin shugabannin kasa da gwamnatocin kasashen yankin Sahel ranar Asabar, 13 ga wtaan Afrilu, 2019.

Wadanda suka raka shugaba Buhari babban filin jirgin saman Djamous domin yi masa bankwana sun hada  jami’an gwamnatin kasar Chadi, ministan harkkin wajen Najeriya, Geofrey Onyeama, ministan harkokin cikin gida na Najeriya, Abdulrahman Dambazzau da ministan tsaro, Mansur Dan-Ali.

Sauran sun hada mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Mohammed Munguno da shugaban hukumar leken asirin Najeriya NIA, Ahmed Rufai Abubakar; shugaban hukumar shiga da ficen Najeriya, Mohammed Babandede; Hajiya Sadiya Umar Farouq da jakadin Najeriya a Chadi, Nasiru Waje.

A kasar Chadi, shugaba Buhari ya yi magana kan yadda makamai ke shigowa Najeriya kuma ke fadawa hannun ya bindiga da suka fara zama kalubale ga zaman lafiyar ‘yan Najeriya.Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga hadin kai a tsakanin kasashen Sahel da Sahara kan yadda za’a shawo kan matsalar.

Leave a Reply