Home Labaru Ilimi Zargin Zamba: Za A Fara Amfani Da Jirage Marasa Matuka A Jarrabawar...

Zargin Zamba: Za A Fara Amfani Da Jirage Marasa Matuka A Jarrabawar JAMB

999
0

Shugaban hukumar shirya jarrabawar share fagen shiga Jami’a ta JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya ce hukumar za ta fara amfani da jirage marasa matuka a lokacin zana jarrabawar shekara ta 2020.

Farfesan ya bayyana haka ne, yayin wani taron masu ruwa da tsaki a jami’ar Ahmadu Bello da ke Kaduna.

Oloyede ya kara da cewa, su na son fito da amfani da jiragen ne, sakamakon yadda wasu mazambata su ka lalata na’u’rorin daukar hoto na sirri da aka kakkafe a cibiyoyin zana jarrabawar.

Farfesa Ishaq Oloyede, ya kuma yi zargin hadin baki da wasu ma’aikatan hukumar wajen lalata na’u’rorin.