Home Labaru Ra’ayi: Ba Laifi Ba Ne Don Miyagu Sun Kewaye Shugaba Buhari –...

Ra’ayi: Ba Laifi Ba Ne Don Miyagu Sun Kewaye Shugaba Buhari – Garba Shehu

513
0
Garba Shehu, Mai Ba Wa Shugaban Kasa Muhammdu Buhari Shawara Na Musamman Kan Harkokin Yada Labarai
Garba Shehu, Mai Ba Wa Shugaban Kasa Muhammdu Buhari Shawara Na Musamman Kan Harkokin Yada Labarai

Fadar shugaban kasa ta ce babu aibu idan akwai miyagu zagaye da Shugaban kasa Muhammadu Buhari, domin akwai irin su a kowace gwamnati a fadin duniya.

Fadar ta kara da jaddada cewa, akwai bukatar a kafa dokar kula da harkokin dandalin sada zumunta na zamani, ganin cewa rashin ta ya na kawo cin zarafi ga mutane.

Mai ba shugaban kasa shawara ta fuskar yada labarai Garba Shehu ya bayyana wa manema labarai haka a labarai a Abuja, inda ya ce babu gwamnatin da aka taba samu a Nijeriya da babu wasu mutane da ake zargi da zama miyagu a cikin ta.

Ya ce irin hakan ya zama wajibi, domin kowace gwamnati ko shugaban kasa ya na da mataimaka ko amintattun makusanta.

Garba Shehu, yace da yawa daga cikin mutanen da ake kira miyagu a gwamnatin shugaba Buhari, mutane ne da su ka samu matukar nasara, kuma su na kokari wajen bauta wa gwamnati, sannan wasu daga cikin su ma ba su da bukatar zama tare da gwamnatin.