Home Labaru Zargin Wuru-Wuru: Kotu Ta Ce Wa Maina Ya Fito Ya Fara Kare...

Zargin Wuru-Wuru: Kotu Ta Ce Wa Maina Ya Fito Ya Fara Kare Kan Sa

120
0

Mai shari’a Okong Abang na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ya ba tsohon Shugaban Kwamitin Gyaran Tsarin Fansho na Nijeriya Abdurrasheed Maina umurnin cewa ya shirya fara kare kan sa a watan Janairu na shekara ta 2021 domin akwai zarge-zarge a kan sa.

Idan dai ba a manta ba, makonni biyu da su ka gabata, Abdurrasheed Maina ya yanke jiki ya fadi a kotu, bayan lauyoyin shi sun shigar da ba’asin cewa bai ci ko sisi ba, don haka babu bukatar bibiyar shi da tuhuma.

Yanzu dai Mai Shari’a Okon Abang ya sanya 26 da 27 ga watan Janairu a matsayin ranakun fara sauraren shari’ar Maina gadan-gadan.