Home Labaru Nuna Damuwa: Zamana A Barcelona Ya Hana Ni Kwazo — Messi

Nuna Damuwa: Zamana A Barcelona Ya Hana Ni Kwazo — Messi

321
0

Lionel Messi ya ce, rashin rabuwar sa da Barcelona ya yi tasiri kan kwazon sa na taka leda a wannan kaka.

A cikin watan Agusta ne dan wasan na Argentina ya yi yunkurin amfani da wani sashi na dokar yarjejeniyar sa da Barcelona don raba gari da kungiyar a matsayin kyauta.

Sai dai Barcelona ta ki amincewa da yunkurin sa, tana mai cewa dole ne a ajiye Euro miliyan 700 kafin sakin dan wasan.

A yayin zantawar sa da gidan talabijin na La Sexta na Sifaniya, dan wasan ya ce, ya yi fama da abubuwa a farkon wannan kaka, amma a yanzu komai ya daidaita a cewar sa.

Gwarzon dan wasan na da damar raba gari da Barcelona kyauta bayan karewar kwantiragin sa a karshen wannan kaka, yayin da yake da ‘yancin fara tattaunawa da wasu kungiyoyi nan da ranar 1 ga watan Janairu mai zuwa.

Leave a Reply