Home Labaru ‘Yan Bindiga Sun Afka Wa Kauye Saboda Kai Karar Su Ga Jami’An...

‘Yan Bindiga Sun Afka Wa Kauye Saboda Kai Karar Su Ga Jami’An Tsaro

67
0

‘Yan bindiga sun kai hari a garin Rogoji da ke karamar hukumar Bakura ta jihar Zamfara, inda su ka kashe mutane biyar.

Da su ke tabbatar da lamarin, mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun kai harin ne domin hukunta su, saboda sun ba jami’an tsaro da ‘yan banga rahoto a kan su.

Majiyoyi sun ce, mazauna yankin sun tallafa wa jami’an tsaro da ‘yan banga wajen kai samame a kan ‘yan bindiga a yankin Lambar Bakura zuwa Dogon Karfe.

Wani mazaunin garin Bakura Hamza Abdullahi, ya ce ‘yan bindigar sun kai hari ne yayin da mazauna garin ke shirin sallar asuba, kuma duk da kalubalantar su da ‘yan banga su ka yi maharan sun shiga cikin garin su ka kashe mutane biyar.