Home Labaru Zargin Rashawa: Yahaya Bello Ya Musanta Tuhuma A Gaban Kotu

Zargin Rashawa: Yahaya Bello Ya Musanta Tuhuma A Gaban Kotu

28
0
Screenshot 20221118 103738 Quick Grid
Screenshot 20221118 103738 Quick Grid

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello tare da wasu mutum biyu da EFCC ta gurfanar a gaban kotu sun musanta zarge-zargen rashawa na Naira biliyan 80 da ake yi musu.

Yahaya Bello, wanda shi ne na farko a cikin mutanen da ake tuhuma tare da sauran mutanen biyu Shu’aibu Oricha da Abdulsalami Hud.

sun musanta duka tuhuma 16 da aka fara karanto musu a gaban mai shari’a Maryanne Anenih ta babbar kotun ta Abuja.

Joseph Daudu, mai mukamin SAN shi ne jagoran lauyoyin da ke kare toshon gwamnan da sauran waɗanda ake tuhuma, yayin da Kemi Pinhero ,ai mukamin SAN, ke jagorantar masu gabatar da ƙara.

Bayan musanta aikata laifukan, lauyan waɗanda ake tuhumar ya nemi a bayar da belin Bello amma lauyan EFCC ya nemi kada a bayar da cewa wa’adi ya wuce tun watan Oktoba.

To amma bayan sauraron ɓangarorin biyu kotun ta tsayar da ranar 10 ga watan Disamba mai kamawa domin duba buƙatar belin.

EFCC ta yi nasarar gurfanar da tsohon gwamnan na jihar Kogi ne a gaban kotun ta tarayya da ke Abuja a jiya Laraba bayan wata da watanni na gaza hakan,

kasancewar ya ƙi amsa gayyatar hukumar kuma duk yunƙurin ta na kama shi ya ci tura.

A ranar Talata ne aka ce tsohon gwamnan ya kai kanshi hukumar ta EFCC da rakiyar lauyoyinsa amma daga baya hukumar ta ce tana tsare da shi.

Leave a Reply