Home Labarai Fatan Mutuwa: Obasanjo Ya Karyata Masu Yada Jita-Jita

Fatan Mutuwa: Obasanjo Ya Karyata Masu Yada Jita-Jita

26
0
IMG 4999 1
IMG 4999 1

Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya ce yana nan da rai kuma yana cikin ƙoshin lafiya, duk da cewa wasu na masa fatan mutuwa.

Da yake magana a garin Osogbo yayin buɗe titin Old-Garage zuwa Oke-Fia da gwamna Ademola Adeleke ya sake ginawa, Obasanjo ya yi magana kan jita-jitar da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta cewa ya mutu.

Ya ce, ya ji jita-jitar cewa ya mutu, kuma ya gani a kafafen sada zumunta inda ya gaggauta sanar da ’ya’yan sa da dangin sa cewa ba gaskiya ba ne kuma yana nan da ran sa.

ya ce waɗanda ke fatan ya mutu burin su kenan, amma Allah ya kare shi.

Obasanjo, ya yaba wa Gwamna Adeleke bisa nasarorin da ya samu a Osun, kuma ya shawarce shi ya ci gaba da gudanar da ayyuka masu kyau.

A nasa jawabin, gwamna Adeleke ya tabbatar wa mutanen Jihar Osun, cewa gwamnatin sa za ta kammala dukkanin ayyukan da ake yi.

Leave a Reply