Home Labarai Kungiyar Afenifere Ta Goyi Bayan Takarar Tinubu

Kungiyar Afenifere Ta Goyi Bayan Takarar Tinubu

318
0

Shugabannin kungiyar yarbawa ta Afenifere sun bayyana goyon bayansu ga Dan takarar shugaban kasa na Jam’iya APC Bola Tinubu.


Shugabannin sun bayyana goyon bayan ne sa’ilinda Tinubu ya kai ziyara a Gidan shugaban kungiyar Afenifere Pa Reuben Fasoranti, ranar Lahadi a Akure, babban birnin jihar Ondo.


Da yake jawabi tsohon sakataren kungiyar ta Afenifere, Cif Seinde Arogbofa, ya dora wa Tinubu nauyin zama jagoran da zai hada kan Nijeriya da samar da ci gaba da ci gaban kasa.


Mataimakin gwamnan jihar Ondo, Mista Lucky Aiyedatiwa, wanda ya tarbi Tinubu da tawagarsa a madadin Gwamna Rotimi Akeredolu, ya ce mutanen jihar Ondo ‘yan ‘Afenifere’ ne kuma za su mara wa Tinubu baya domin ya samu nasara.


Shima, Gwamna Biodun Oyebanji na Ekiti ya tabbatar wa shugabannin Yarbawa cewa dukkan gwamnonin Kudu maso Yamma da jama’a na goyon bayan Tinubu.


Tsohon sakataren gwamnatin tarayya kuma jigo a kungiyar Afenifere Cif Olu Falae, Bola Tinubu ya yi kokarin gyara tattalin arzikin kasar nan idan ya samu nasara.


Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya rawaito cewa shugabannin kungiyar Afenifere na jihohin Kwara da Kogi sun hallara a gidan jagoran Afenifere domin bayar da goyon baya ga Asiwaju Tinubu.

Leave a Reply