Home Labaru Zargin Boye Shekaru: Kotu Ta Yi Watsi Da Karar Da Aka Shigar...

Zargin Boye Shekaru: Kotu Ta Yi Watsi Da Karar Da Aka Shigar Kan Tanko Muhammad

281
0
Ibrahim Tanko Muhammad, Shugaban Alkalan Najeriya

Babbar kotun tarayya dake Abuja ta yi watsi da karar da aka shigar gabanta bisa zargin mai rikon mukamin shugaban alkalan Najeriya da karya wajen bayyana shekarunsa.


Mai shari’a Danlami Senchi wanda ya jagoranci shari’ar ya ce karar da wani Tochi Micheal ya shigar a watan Afrailu bata cancanci a ci gaba da sauraronta ba.


A cewar alkalin ba wasu shaidu da mai shigar da kara ya gabatar dake tabbatar da zarginsa na cewa shugaban alkalan ya rage shekaru daga 31 ga watan Disambar 1950, zuwa 31 ga watan Disambar 1953.


Senchi ya ce bincike ya tabbatar da cewa an haifi wanda ake karar ne a ranar 31 ga watan Disambar 1953 ba 31 ga watan Disambar 1950 ba kamar yadda mai shigar da kara ya yi zargi.


Sannan ya bukaci magatakardar kotun da ya fara hukunta bangaren masu kare karar da aka shigar sakamakon sanyo bayanai da basu da tabbaci a kai.