Kotun daukaka kara dake Legas, ya amincewa bukatar hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC na kwace sama da naira billiyan 1 na Paris Club da kungiyar gwamnonin Najeriya ta ba wani kamfani.
Ana dai danganta kamfanin ne da shugaban majalisar dattawa mai barin gado Bukola Saraki, wanda tuni hukumar ke tuhumar wasu na hannun damarsa da suka hada da Gbenga Makanjuolu, da Kolawole Shittu.
A ranar 27 ga watan Afrailun shekarar da ta gabata ma mai shari’a Cecelia Olatoregun ta amince da a kwace kudaden tare da damkasu ga gwamnatin tarayya.
Rashin gamsuwa da shari’ar ya sa kamfanin ya garzaya kotun koli domin kalubalantar matsayar da aka cimma.