Kwamitin Majalisar Wakilai kan yaƙi da cutar maleriya da
kanjamau da tarin fuka, na neman Ministan Lafiya,
Farfesa Muhammad Ali Pate da ya bayyana a gabanta
kan zargin almundahanar dala miliyan 300.
Ministan tare da sakatariyar ma’aikatar, Daju Kachollom za su bayyana a gaban majalisar ne bisa zargin karkatar da maƙudan kuɗin da aka tanada domin yakar cutar maleriya tun a shekara 2021.
Shugaban kwamitin, Amobi Godwin Ogah ya kuma ce mutanen biyu za su ba da bahasi kan wani zargin da ake yi musu na hana masana’antun cikin gida kwantiragin samar da gidajen sauro masu magani da sauran kayayyaki.
A cewar shugaban kwamitin, a shirye suke su sanya a kamo sakatariyar bisa kin amsa gayyatar majalisar da ta yi har sau uku a jere.
An samar da kudin nan tun a 2021, kuma mun sha gayyatar sakatariyar ma’aikatar amma shiru kake ji. Kazalika, Ogah ya ce majalisar ta bai wa ministan da sakatariyarsa wa’adin sa’o’i 72 domin gabatar da kansu a gaban kwamitin, ko su fuskanci fushinsu.