Ministan shari’ar Najeriya ya bayyana takaici kan yadda ya ce wasu ‘yan siyasa na kange kan su daga kamu bisa wasu laifuka da ake zargin sun aikata.
Chief Lateef Olasunkanmi Fagbemi SAN ya bayyana hakan ne biyo bayan kulli-kurciyar da aka yi tsakanin tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello da jami’an hukumar EFCC inda a ‘karshe suka kasa kama shi sakamakon kange shi da ake zargin wani jami’in gwammnati ya yi.
Al’amarin ya sanya minstan shari’a ya gargadi jami’an gwamnati wadanda dokar ‘kasa ke karewa su guji kawo cikas a kokarin da ya cancanci yabo da hukumar EFCC ke yi.
Shima mai sharhi, Barrister Audu Bulama Bukarti ya bayyana cewar akwai bukatar a sani wannan abu ne da ya zama wajibi, ya ce hukumar EFCC, hukuma ce da dokar Najeriya ta kafa ta kuma ta bata ikon ta binciki wanda ake zargi da laifi komai girman sa a ‘kasa.
Barrista Bulama ya kuma kara da cewa a dokokin Najeriya, kokarin kange wanda hukuma take nema babban laifi ne da doka ta tanadar wa hukuncin zaman gidan kurkuku na shekara biyar ba tare da zabin tara ba.