Home Labaru Zargin Badaƙalar Da Atiku Ya Yi Min Lokacin Zaɓe, Ko a Shari’a...

Zargin Badaƙalar Da Atiku Ya Yi Min Lokacin Zaɓe, Ko a Shari’a Ba Ta Da Tushe –Tinubu

1
0

Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya ce zargin
da Atiku Abubakar ya yi ma shi na “harƙalla” a lokacin zaɓen
shugaban ƙasa ba ya da hurumi a shari’a ko kaɗan.

Tinubu ya bayyana wa kotu haka ne, ya na mai cewa babu inda a cikin ƙorafin da Atiku ya shigar a kotu ko ya yi bayanin wurare ko wurin da ya ce an yi harƙallar.

Atiku Abubakar da jam’iyyar PDP dai sun garzaya kotu, su na roƙon a soke zaɓen ko kuma a ba Atiku nasara, bisa ga zargin ɗibga maguɗi da su ka ce an yi a zaɓen na ranar 25 ga Fabrairu.

APC da Tinubu sun maida wa Atiku da PDP raddi, cewa ba su da wata hujjar da za su nemi kotu ta umarci hukumar zabe ta sake zaɓe ko kuma ta ƙwace nasarar da su ka yi ta ba Atiku da PDP.

Babban Lauyan Tinubu Wole Olanipekun, ya ce zargin da Atiku ke yi cewa an ƙi bin Dokar Zaɓe ta shekara ta 2022 ba ya da tushe ko hujja.