Hukumar EFCC da ke yakar rashawa ta cafke Hafsat Ganduje uwargidan gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje kan zargin rashawa da zambar fili wanda ɗanta ya kai kararta.
Kama matar Ganduje na zuwa ne makonni bayan kin amsa gayyatar hukumar ta EFCC.
Tun a ranar 13 ga watan Satumba kafafan yaɗa labarai a Najeriya suka rawaito cewa EFCC ta tura wa Hafsat Ganduje goron-gayyata.
Wata majiya mai karfi daga gidan gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da cafke Hafsat Ganduje a yammacin jiya Litinin, sai dai an shaida cewa ta koma gida.
Idan ba’a manta ba dai,dƊan Hafsat Ganduje ne Abdualzeez Ganduje ya kai karar mahaifiyarsa gaban EFCC.