Matakin da Gwamnatin Jihar Kaduna ta dauka na hana safarar itace da gawayin girki ya sanya talakawa cikin damuwa.
A makon jiya ne gwamnatin jihar ta haramta safarar itace da gawayi da hawa babura a fadin jihar a matsayin matakan tsaro, lamarin da ya sanya akasarin al’ummar jihar cikin kunci, musamman talakawa.
Malam Zubairu Sani mazaunin Anguwar Tudun Jukun Zariya, ya ce, sun san cewa haka lamarin yake ba sai ga shi sun shiga wani hali na lahaula wala kuwata domin kusan duk wani abu da dan Adam zai rayu da shi yana dab da ya kubuce musu.
Daga bisani “Al’ummar sun yi kira ga Gwamnan Nasiru El-Rufai da ya duba halin da talakawa ke ciki da kuncin rayuwa da matsin tattalin arziki ya haifar, ya kyale masu babura wadanda ba na haya ba su yi amfani da abinsu.