Home Labaru Zargi: NPF Sun Cusa Sunayen Kurata 925 A Jerin Sababbin Jami’an ‘Yan...

Zargi: NPF Sun Cusa Sunayen Kurata 925 A Jerin Sababbin Jami’an ‘Yan Sanda — PSC

249
0

Hukumar kula da harkokin ‘yan sanda ta Nijeriya, ta ce mutane
925 aka cusa ta bayan fage a cikin jerin sababbin kananan
jami’an da za a dauka aiki.

Wata majiya ta ce, hukumar ta na zargin shugaban rundunar
‘yan sandan Nijeriya Mohammed Adamu da yin wannan danyen
aiki da ya saba wa doka.

Ta ce mutane 900 da aka ba aiki ba su shiga cikin masu neman
zama ‘yan sanda ba, sannan ba a yi masu gwaji ko wata irin
tantancewa ba.

Hukumar ta bayyana wannan ne, yayin da ta ke musanta zargin
da ake yi mata na hana wasu jami’an ‘yan sanda da aka dauka
aiki a shekarar da ta gabata kudaden su.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ta Ikechukwu
Ani, hukumar ta ce babu dan sandan da aka hana kudin sa.

Ikechukwu Ani, ya ce duk wadanda aka dauka aiki sun samu
takarda kuma an tantance su, an kuma yi masu rajista da tsarin
albashi na IPPIS, ana kuma jiran gwamnatin tarayya ta fara
biyan su.