Home Home Zan Yi Nazari A Kan Buƙatar Sakin Nnamdi Kanu – Buhari

Zan Yi Nazari A Kan Buƙatar Sakin Nnamdi Kanu – Buhari

173
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce zai yi nazari a kan buƙatar neman ya saki Nnamdi Kanu da ƙungiyar dattawan al’ummar Ibo su ka gabatar ma shi.

Buhari ya bayyana haka ne, yayin da ya karbi baƙuncin
dattawan a fadar sa da ke Abuja, a ƙarƙashin jagorancin tsohon
Ministan Sufurin Jirgin Sama Mbazulike Amaechi.

A cikin wata sanarwa da Kakakin sa Femi Adesina ya fitar,
Buhari ya ce dattawan sun nemi abu mai matuƙar girma a
matsayin shi na shugaban ƙasa.

Ya ce buƙatar da dattawan su ka nema ta saɓa wa tanadin tsarin
mulki, wanda ya fayyace tsarin shugabanci tsakanin gwamnati
da ɓangaren shari’a.

Shugaba Muhammadu Buhari, ya ce buƙatar da dattawan su ka
gabatar mai girma ce sosai, amma zai yi nazari a kan ta.