Home Labaru Zan Yi Aiki a Bayyane Tare Da Shugabannin Majalisa Ta 10 –...

Zan Yi Aiki a Bayyane Tare Da Shugabannin Majalisa Ta 10 – Tinubu

276
0

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya yaba da zaben
Godswill Akpabio da Tajudeen Abbas a matsayin shugaban
majalisar dattawa da na wakilai, inda ya tabbatar da cewa zai
yi aiki tare da sabbin shugabannin.

Tinubu ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, inda ya bayyana nasarar shugabannin majalisar biyu da mataimakan su a matsayin babban ci-gaban da aka samu a dimokradiyyar Nijeriya.

Ya ce a matsayin shi na shugaba a shirye ya ke ya yi aiki tare da majalisar dokoki ta kasa a bayyane.

‘Yan Nijeriya dai su na sa ran sanatoci da ‘yan majalisar wakilai za su kafa dokoki da gudanar da ayyukan da za su inganta ayyukan gwamnati domin samun sakamako mai kyau ciki har da inganta rayuwars u.

A karshe ya jajenta wa Abdulaziz Yari da Idris Wase da Aminu Jaji bayan sun fadi zabe, inda ya bukaci su cigaba da gajircewa kamar yadda su ka yi a takarar shugabancin majalisar wajen gudanar da ayyukan su ga al’ummar mazabar su da ma Nijeriya baki daya.

Leave a Reply