Home Labaru Zamu Kammalawa Yankin Yarbawa Manyan Tituna Biyu A Shekarar Nan – Buhari

Zamu Kammalawa Yankin Yarbawa Manyan Tituna Biyu A Shekarar Nan – Buhari

82
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa za a kammala manyan tituna biyu da ake kan ginawa a yankin kudu maso yammacin Nijeriya kafin karshen shekara ta 2022.

Manyan titunan kuwa sun hada da ta Shagamu zuwa Benin, da kuma Legas zuwa Ibadan.

Mai magana da yawun Shugaban kasa Femi Adesina, ya ce Buhari ya bada tabbacin ne yayin da ya kaddamar da manyan ayyuka biyar a jihar Ogun.

Manyan ayyukan da shugaba Buhari ya kaddamar a jihar Ogun dai sun hada da Babban titin Sagami zuwa Abekuta mai tsawon kilomita 42, da Titin Ijebu-Ode-Epe mai tsaywon kilomita 14, da  Rukunin gidaje na Kobape da wasu a Oke-Mosan.