Home Labaru Jirgin Qatar Airways Zai Fara Sauka Da Tsahi A Kano

Jirgin Qatar Airways Zai Fara Sauka Da Tsahi A Kano

89
0

Gwamnatin tarayya ta ba kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Qatar Airways damar fara sauka da tashi daga filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano da ke Jihar Kano.

A Cikin wani saƙon da ya wallafa a shafin sa na Twitter, kamfanin Qatar Airways ya ce an kuma ba shi damar sauka a filin jirgi na Fatakwal da ke Jihar Rivers.

Rahotanni sun ce, Kamfanin Qatar zai fara jigilar jirage a Kano da Fatakwal ne a farkon watan Maris na shekara ta 2022.