Home Home Zaman Lafiya: Shugabannin Afirka Za Su Dakatar Da Buɗe Wuta a Gabashin...

Zaman Lafiya: Shugabannin Afirka Za Su Dakatar Da Buɗe Wuta a Gabashin Congo

44
0

Shugabannin Afirka sun ayyana dakatar da buɗe wuta daga gobe Juma’a a gabashin Congo inda ‘yan tawayen kungiyar M23 ke ta samun gagarumar nasara a watannin nan.

Wannan na dauke ne a wata sanarwa da aka fitar a karshen wani karamin taron koli a babban birnin Angola, Luanda, wanda ministan harkokin waje na Rwanda da shugabannin kasashen Jamhuriyar Dumukuradiyyar Kongo da Angola da kuma Burundi suka halarta.

Wadanda suka sanya hannu a sanarwar sun amince cewa dakarun haɗaka na wanzar da zaman lafiya na kasashen Gabashin Afirka, za su kai hari duk wuraren da mayakan kungiyar M23 suke, idan har ‘yan tawayen ba su janye daga yankunan da suka mamaye ba, nan da nan.