Home Labaru Katinan Zabe 200,000 Ne Ba A Karba Ba A Adamawa —INEC

Katinan Zabe 200,000 Ne Ba A Karba Ba A Adamawa —INEC

319
0

Yayin da ya rage kasa da kwanaki 100 kafin zaben shekara ta 2023, Hukumar Zabe ta Kasa ta koka da yadda jama’a ke kin zuwa karbar katin zaben su.

Sabon Kwamishinan hukumar zabe na Jihar Adamawa Hudu Yunusa, ya nuna damuwar sa a kan tarin katunan zaben da ke jibge a ofishin su, inda ya ce sama da katin zabe dubu 200 ke zube a ofisoshin su ba tare da an zo an karba ba.

Ya ce katunan na masu zaben da aka yi wa rijista ne tun daga shekara ta 2019, a tsakanin kananan hukumomi 21 da jihar ke da su.

Hudu Yunusa, ya ce an samu karin masu zabe dubu 36 da aka yi wa rijista a shekara ta 2022.

Daga nan, ya bukaci wadanda su ka san sun yi rijista ba su karbi katin zaben su ba, su kokarta su je su karba tun kafin lokaci ya kure.

Leave a Reply