Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar Abuja zuwa Daura a jiharsa ta haihuwa Katsina, domin yin rijistar jam’iyya da kuma sabunta zamansa mamba a jam’iyyar ta APC.
Kamfanin dillancin lbarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa shugaban kasan ya bar Abuja ne bayan idar da sallar Juma’a a masallacin fadar shugaban kasa.
A yau Asabar ne ake sa ran shugaban kasan ya je mazabar Sarkin Yara a Daura, domin sabunta katin sa na dan jam’iyyar APC da misalin karfe 12 na rana.
A ranar Alhamis ne daraktan jam’iyyar Farfesa Ussifu Medaner ya ce babu wakilci a aikin sabunta katin zama dan jam’iyyar.
Ya ce wannan aiki na da matukar mahimmanci kuma akwai wasu abubuwa na daban da yake da su wadanda za a fuskanta a zabuka nan gaba.
Medaner, ya ce akwai bukatar kowa ya je da kansa domin yin wannan rijista, yana jaddada cewa ba za su amince da wakilci ba.
You must log in to post a comment.