Home Labaru Zabukan 2023: Jam’iyyar PDP Na Shirin Babban Taro Na Zaben Sabbin Shugabanninta

Zabukan 2023: Jam’iyyar PDP Na Shirin Babban Taro Na Zaben Sabbin Shugabanninta

73
0

Bisa dukkan alamu rigimar cikin gida da ke addabar babbar jam’iyyar hamayya ta PDP na ci gaba da yi mata tarnaki, yayin da a bangare guda shugabanninta da sauran masu fada a ji suke kokarin dinke barakar.

Kwamitin amintattun jam`iyyar ya yi wani zama na musamman a ranar Talata, inda ya bude zaurensa ga jiga-jigan jam`iyyar da kuma duka gwamnonin jam`iyyar su 13.

Sun tattauna a kan rikicin da ya dabaibaye jam`iyyar ne wanda ya ta’azzara musamman bayan da wadansu mataimaka ga `yan kwamitin gudanarwar jam`iyyar su bakwai suka yi murabus.

Dalilin murabus din shi ne ba su gamsu da jagorancin shugaban jam`iyyar na kasa, Uche Secondus ba, suna zarginsa da rashin iya shugabanci, suna kuma bukatar lallai ya sauka daga mukaminsa.