Home Labaru Ilimi Inganta Ilimi: Zulum Ya Shammaci Wasu Malaman Firaimare Da Jarabawar Ba-Zata

Inganta Ilimi: Zulum Ya Shammaci Wasu Malaman Firaimare Da Jarabawar Ba-Zata

63
0

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi wa wasu malaman makarantar firaimare da ke garin Baga jarabawar ba-zata.

Zulum ya yi wa malaman jarabawar ne don a gwada cancantarsu a fannin koyarwa a cewar wata sanarwa da gwamnatin jihar ta wallafa a shafinta na sada zumunta.

Gwamna na ziyarar aiki ne a garin na Baga wanda ya yi fice a harkar sana’ar su a yankin Tafkin Chad, inda har ya kwana daya a garin.

“Zulum ya fadawa malaman cewa, ba an gudanar da jarabawar ba ne don a kori wani malami a aiki, sai dai don a auna kwarewarsu don a san inda za a saka su, ya kara da cewa, wadanda ba su da kwarewa a fannin koyarwar, za a ba su zabin a mayar da su wata ma’aikata ko kuma a tura su su karo ilimi.