Jinkiri da mahukunta suke yi wurin nadin sabon sarkin Zazzau na ci gaba da jawo cece-kuce da kuma yada labarai mabanbanta game da masarautar, ciki har da maganar rarraba masarautar zuwa gida uku.
A baya-baya nan Bayanin gwamnan jahar Kaduna Malam Nasiru El-rufa’i yayi a wajen gabatar da kasafin kudin badi gaban majalisa, ya kara karfafa jita-jitar raba masarautar.
To sai dai Sai dai kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jahar Malam Samuel Aruwan ya musanta wannan rade-radi.
Ita ma dai majalisar dokokin jihar Kaduna ta ce babu wani kudurin doka game da raba masarautar Zazzau kamar yadda Dan-majalisar mai wakiltar Zaria a majalisar Sulaiman Ibrahim Dabo, ya tabbatar a shafinsa na sada zumunta.
Tuni dai aka jibge jami’an tsaro a bakin fadar sarkin Zazzau domin gudun abin da ka iya tasowa.
You must log in to post a comment.