Home Labaru Sufurin Ruwa: Najeriya Za Ta Haramtawa Jirage Marasa Rijista Shawagi

Sufurin Ruwa: Najeriya Za Ta Haramtawa Jirage Marasa Rijista Shawagi

208
0

Hukumar kula da sufirin ruwa ta Kasa ta bai wa jiragen dake jigila wa’adin watanni 3 domin su kammala rijista tare da sabunta lasisi.

A wata sanarwar da Hukumar ta NIMASA ta fitar ta ce za ta sanar da kamfanonin man ketare da kada suyi mu’amala da duk wasu kamfanonin da basu yi rijista da hukumar ba.

Rahotanni sun tabbatar da cewa mafi yawancin jiragen da ke shawagi a ruwan kasar nan mallakin ‘yan kasuwa ne, kuma suna aikin safarar danyen man fetur ne zuwa kasashen duniya.

Kazalika Sanarwar ta ce wa’adin na watanni 3 ya shafi kamfanonin da ke da rijista amma wa’adin lasisinsu ya kare.

Matakin dai na zuwa ne a wani mataki na kokarin da gwamnati ke yi na ganin ta kara fadada hanyoyin samun kudadem shiga da kuma samun kudaden musaya daga kasashen ketare.

Bayanai sun tabbatar da cewa akasarin jiragen ruwan kasashen ketare ne suka mamaye harkokin sufurin mai a kasar nan, kuma bincike ya tabbatar dad a cewa da dama daga cikin su ba su da cikakken lasisi yayinda wasun su basa biyan haraji kamar yadda da doka ta tanada ba.