Home Labaru Zaben Nasarawa: Al-Makura Ya Sake Yin Nasara A Kotun Daukaka Kara

Zaben Nasarawa: Al-Makura Ya Sake Yin Nasara A Kotun Daukaka Kara

474
0
Sanata Umar Tanko Al-Makura
Sanata Umar Tanko Al-Makura

Kotun daukaka kara da ke zama a Makurdi, ta ba Sanata Umar Tanko Al-Makura nasara, biyo bayan hukuncin da ta yanke a kan karar da Sanata Suleiman Adokwe na jam’iyyar PDP ya shigar.

Alkalan kotun Mai shari’a Jummai Hannatu Sankey da Joseph Eyo Ekanem, sun yi watsi da karar da aka shigar ana kalubalantar zaben gwamnan jihar.

Daya daga cikin alkalan Sanata Al-Makura Mubarak Tijani Adekilekun, ya ce ya yi farin ciki da hukuncin kotun, kuma tabbatar da nasarar Al-Makura nasara ce ga Demokradiyyar Nijeriya.

Da yak e zantawa da manema labarai bayan yanke hukuncin, Sanata Suleiman Adokwe ya ce wannan kaddara ce ta Allah, don haka ya na godiya ga Allah da ya ba shi ikon amincewa da hukuncin kotun cikin kwanciyar hankali.

Idan dai ba a manta ba, Hukumar Zabe Mai Zaman Kan ta ta kasa ta bayyana Al-Makura a matsayin wanda ya lashe zaben Dan Majalisar Tarayya a watan Fabrairu na shekara ta 2019, bayan ya samu kuri’u dubu 113 da 156, inda ya doke Adokwe na jam’iyyar PDP da ya samu kuri’u dubu 104 da 595.