Hukumar zaben Najeriya ta ce babu gudu babu ja da baya dangane da shirin gudanar da zaben gwamnan jihar Anambra da ake saran gudanar da shi ranar 6 ga watan Nuwamba duk da barazanar dake zuwa daga kungiyar ‘Yan awaren IPOB na hana zaben.
Hukumar zaben tace tana ci gaba da shirye shiryen da suka kamata wajen ganin ta kammala tsarin da ya dace na gudanar da karbabben zabe, ciki harda ganawa da hukumomin tsaron da ake saran su kare lafiya da kuma dukiyoyin jama’a.
Shugaban Hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ya ce babu dalilin ‘dage shirin gudanar da zaben domin sun tattauna akan irin barazanar da suke fuskanta da kuma hanyoyin da ake saran shawo kan su.
Yakubu wanda ya bayyana takaicin sa akan yadda ake ci gaba da fuskantar rasa rayuka da kuma kadarori sakamakon ayyukan ‘Yan awaren, yace ganawar da suka yi da bangarori da dama a Jihar Anambra ta nuna musu bukatar ci gaba da shirin gudanar da zaben wanda za’ayi a ranar 6 ga watan gobe.
Shugaban Hukumar zaben yace zasu ci gaba da aiki tare da hukumomin tsaron kasa wajen gudanar da ayyukan su da kuma kare kayan aikin su, lura da yadda ake ci gaba da kai musu hare hare ana lalata su.
Ana saran Hukumar ta gabatar da kundin masu gudanar da zabe a ranar 7 ga wannan wata tare da kuma gabatar da sunayen ‘Yan takarar da aka tantance.