Home Labaru Afghanistan: ‘Ya’ya Mata Sun Fara Zuwa Makarantun Sakandare

Afghanistan: ‘Ya’ya Mata Sun Fara Zuwa Makarantun Sakandare

221
0

Rahotanni daga kasar Afghanistan na cewa  ‘yan mata sun koma wasu makarantun sakandare a lardin arewacin kasar, sai dai kamar yadda wasu jami’an Taliban suka bayyana, har yanzu dokar haramta musu halartar ajujuwa na aiki a sassa da dama na kasar.


Sabuwar gwamnatin mai tsattsauran ra’ayi ta kuma sanar a wani taron gangami da aka gudanar cewa an kira wasu mata ma’aikatan gwamnati da su koma bakin aiki kuma za a biya su albashi, alamun kungiyar na kokarin yiwa al’umma sassauci bayan kwashe kwanaki hamsin a kan madafun iko.


Bidiyon da kakakin kungiyar Suhail Shaheen ya wallafa ya nuna ‘yan mata’ yan makaranta da dama cikin bakaken kaya, wasu sanye da fararen mayafi wasu kuma da mayafin fuska, suna zaune kan kujeru suna daga tutar Taliban.
Amma a Kabul, jami’in ma’aikatar ilimi Mohammad Abid ya ce babu wani sauyi na siyasa daga gwamnatin rikon kwarya ta Taliban, inda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa har yanzu ba a ba wa mata ikon halartar manyan makarantu ba.


A watan da ya gabata kakakin kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid ya shaida wa wani taron manema labarai cewa ana ci gaba da aiki kan batutuwan ilimi da aikin mata, yana mai cewa za a bude makarantu, sai dai bai bayyana takamammen lokacin da za a bude din ba.

Leave a Reply