Akwai yiwuwar jam’iyyar hamayya ta PDP za ta tsaida ‘dan takarar ta na shugaban kasa a zaben 2023 ne daga Arewacin kasar nan.
A zaman majalisar zartaswa ta PDP ta yi a karshen mako, jam’iyyar ta ce za ta fito da tsarin da za a bi wajen nada sababbin shugabanni.
Akwai jiga-jigan adawa da suke harin kujerar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar ta PDP, kuma mafi yawansu sun fito ne daga jihohin Arewacin Najeriya.