Home Labaru Zaben 2023: Kungiyoyin Arewa 60 Sun Ce Ba Su Goyon Bayan A...

Zaben 2023: Kungiyoyin Arewa 60 Sun Ce Ba Su Goyon Bayan A Maidawa ‘Yan Kudu Mulki

84
0

Gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya, ta nuna adawarta ga tsarin karba-karba da jam’iyyun siyasa suke kawo wa yayin da ake shirin zabe.


Mai magana da yawun kungiyar Abdul-Azeez Suleiman, ya bayyana cewa wannan tsarin ya saba dokar kasa, kuma yunkuri ne na murkushe ‘yan Arewa.


A wajen taron manema labarai Abdul-Azeez Suleiman, ya ce an kawo wannan batu ne da nufin a hana Arewa takara a zaben 2023.


Suleiman ya yi kira ga jam’iyyun siyasar kasar nan su yi watsi da maganar karba-karba da kuma kai tikitin takarar shugaban kasa zuwa kudancin kasar nan a 2023.


Ya ce Gamayyar kungiyoyi 60 a karkashin ta, ta na so duk jam’iyyu su yi koyi da gwamnonin Arewa da suka dauki matsayar cewa karba-karba ya saba doka.


A cewar sa, mutanen Arewa ba za su yarda da wani shiri na hana su neman kujera a zabe mai zuwa ba.