Home Labaru Zaben 2023: Gwamnatin Tarayya Ta Ware Naira Billiyan 100

Zaben 2023: Gwamnatin Tarayya Ta Ware Naira Billiyan 100

21
0

Gwamnatin tarayya ta ware zunzurutun kudi har naira biliyan 100 domin gudanar da babban zaben shekarar 2023.


Gwamnatin ta kara kasafin kudin kasa na shekarar daga naira tiriliyan 13.98 zuwa naira triliyan 16.45, wanda ke nuna cewa an samu karin tiriliyan 2.47.


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika wa Majalisar Wakilai don amincewa, sannan kuma ya kasance na shekara-shekara, yana jujjuya tsarin kashe kudi na shekaru uku wanda ke ba da fifikon kashe kuɗi na matsakaicin lokaci da taƙaitaccen kasafin kuɗi wanda za a iya haɓaka tsare-tsaren bangare da tsaftace su..


A kwanakin baya ne majalisar ta zartar da na farko mai dauke da tiriliyan 13 da billiyan 98 na kasafin kudin kasa na 2022.
Amma a cikin wata wasika mai kwanan wata 2 ga Oktoba, 2021 da aka aika wa shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila, Shugaba Buhari ya ce bukatar yin la’akari da sabbin sharuddan kasafin kudi a cikin dokar masana’antar man fetur a 2021, da sauran muhimman kashe-kashe a cikin kasafin kudi na 2022 ya zama dole a sake nazari.