Home Labaru Ta’addanci: An Yi Wa Jami’In DSS Kisar Gilla A Jihar Imo

Ta’addanci: An Yi Wa Jami’In DSS Kisar Gilla A Jihar Imo

25
0

An yi wa jami’in hukumar yan-sandan farin kaya DSS, kisar gilla a garin Owerri, babban birnin jihar Imo.
Hakan na faruwa ne kasa da awa 48 bayan kona ofishin hukumar da aka yi a Nnewi, na jihar Anambra.


An bindige jami’in hukumar mai suna Prince Nwachinaemere a karamar hukumar Owerri ta kudu a hanyar Onitsha.
An tura jami’in ya yi wani aiki ne a Anambra awanni kadan bayan kona ofishin DSS na Nnewi, inda aka kashe shi a lokacin da ya ke hanyarsa ta komawa wurin aikin sa.


A halin yanzu babu cikakken bayani kan yadda ya mutu duba da cewa wani rahoton ya ce ya mutu ne sakamakon kuskuren harbi.
Daya daga cikin yan uwansa, Deacon Daniel Opara, wanda ya tabbatar da rasuwarsa ya bayyana lamarin a matsayin abin bakin ciki.