A ranar Talatar nan ne ake sa ran tawagar tarayyar kasashen Turai da ta yi aikin sa-ido a kan zaben Nijeriya, za ta mika rahoton ta na karshe da ta tattara a kan zabubbukan da aka gudanar ga shugaban majalisar dattawa sanata Ahmed Lawal.
Rahoton tarayyar Turai dai ya zargi Jam’iyyun siyasa da tunzura tashin hankalin da ya kai ga rasa rayuka da kuma jikkata mutane, yayin da ya zargi jami’an tsaro da kasa daukar matakan kare lafiyar jama’a da dukiyoyin su.
Idan dai ba a manta ba, a farkon watan Yuni ne kungiyar Kare Hakkin Bil-Adama ta Human Rights Watch, ta ce hare-hare da tashin hankali sun mamaye zaben shugaban kasa na wannan shekarar, yayin da ta zargi jami’an tsaro da hannu wajen haddasa matsalolin da aka samu.
Kungiyar ta ce, ‘yan bindiga sun kai farmaki a kan masu kada kuri’u da ‘yan jarida da masu sa-ido a zaben, musamman a jihohin Rivers da Kano.