Home Labaru Siyasar Kogi: Zaben Fidda Gwani Ya Raba Kan Shugabannin APC

Siyasar Kogi: Zaben Fidda Gwani Ya Raba Kan Shugabannin APC

416
0
APC
APC

Wasu daga cikin manyan jam’iyyar APC a jihar Kogi, sun bukaci uwar-jam’iyyar ta sa baki wajen ganin an yi amfani da tsarin kato-bayan-kato a zaben tsaida dan takarar gwamna.

Rahotanni sun ce, wasu daga cikin masu fada a ji na jam’iyyar APC su na so jam’iyyar ta yi ‘yar-tinke wajen fito da wanda zai tsaya takara.

Kusoshin jam’iyyar dai sun shimfida bukatar hakan ne, yayin da aka shirya wani taron masu neman kujerar gwamna a jihar, inda ‘yan takara 17 daga cikin 20 su ka halarta a Abuja.

Sanata Alex Kadiri, ya ce sun shirya taron ne bayan samun labarin cewa, wani haramtaccen kwamiti da aka nada na yaran Yahaya Bello su na kokarin ganin an yi amfani da wakilan jam’iyya wajen tsaida dan takara.

Ta ce dole a yi amfani da tsarin zabe na kato-bayan-kato, inda kowane dan jam’iyya daga cikin kananan hukumomin jihar zai fito ya zabi dan takarar da ya ke so.

Leave a Reply