Atiku Abubakar da jam’iyar PDP sun bukaci kotun sauraren korafe-korafen zabe ta binciki kayayyakin da hukumar zabe mai zaman kanta ta yi amfani aiki da su a zaben 2019.
Jam’iyar ta PDP na cigaba da ikirarin cewa, ita ce ta yi nasara a zaben shugaban kasa da ya gabata ba wai jam’iyyar APC ba.
PDP ta roki kotun sauraren korafe-korafen zabe da ta ba su damar binciken shafin yanar gizo na hukumar zabe ta kasa INEC, sannan ta roki kotun ta ba su damar binciken na’urorin zamani wadanda aka yi aiki da su a zaben shugaban kasa na ranar 23 ga watan Faburairu.
Kamfanin dillacin labarai na kasa NAN ta ruwaito cewa, cikin korafin da Atiku da jam’iyar PDP suka shigar gaban kotun ya hada da cewa, jam’iyar su ce ta lashe zaben shugaban kasa, bisa sakamakon da su kace yana nan kunshe a shafin yanar gizon INEC.
Sai dai hukumar INEC ta karyata wannan zance da jam’iyar PDP ta yi game da sakamakon zaben ranar 23 ga watan Faburairun 2019, wanda ta yi ikirarin cewa ta samo daga shafin yanar gizon hukumar.