Home Labaru Shugabanci: PDP Ta Yi Wata Ganawa Domin Zaben Shugabannin Marasa Rinyaye A...

Shugabanci: PDP Ta Yi Wata Ganawa Domin Zaben Shugabannin Marasa Rinyaye A Zauran Majalisu

350
0

Kwamitin gudanar wa na jam’iyyar PDP ya yi wata ganawa ta musamman domin zaben shugabannin marasa rinjaye a majalisun tarayyar Nijeriya.

PDP dai, ta sa ranar da zata zabi mai tsawatarwa na bangaren marasa rinjaye a zauran majalisun biyu da kuma shugaban ‘yan majalisar da aka zaba a karkashin inuwar jam’iyyar PDP.

shugaban jam’iyyar PDP na kasa Uche Secondus ya jagoranci gudanar da taron wanda ya samu halartar daukacin Sanatoci da ‘yan majalisar wakilai da kuma mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar.

Idan dai za a iya tunawa, tun kafin gudanar da wannan taro, jam’iyyar PDP ta gana domin tsara yadda za a zabi shugabannin marasa rinjaye da sauran mukaman ba tare da samun wata matsala ba.

Ana dai zaton cewa, jam’iyyar PDP na son ta ba sanata Philiph Aduda shugaban marasaa rinjaye, sannan ta ba sanata Enyinnaya Abaribe mukamin mai tsawatarwa na marasa rinjaye a zauran majalisar dattawa.

Leave a Reply