Shugaban hukumar , ya ce sai an yi wa kowani ɗan takara a zaɓen ƙananan hukumomin jihar da za a yi gwajin ƙwaya kafin a bashi damar tsayawa takara.
Farfesa Malumfashi, ya sanar da hakan ne a yayin wani taron manema labarai da hukumar ta gudanar a Kano a Alhamis din nan.
A yayin taron, hukumar zaben ta sanar da cewa duk mai son tsayawa takarar shugaban ƙaramar hukuma a zaɓen to zai sayi takardar cikewa wato Foam a kan naira miliyan 10,
yayin da ɗan takarar kansila kuma kuɗin takardar cikewar sa ya kama naira miliyan biyar.
Za a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar ne dai a ranar 30 ga watan Nuwambar 2024.