Home Labaru Zababben Dan Majalisar Jiha Mai Wakiltar Chikun Ta Jihar Kaduna Ya Rasu

Zababben Dan Majalisar Jiha Mai Wakiltar Chikun Ta Jihar Kaduna Ya Rasu

289
0

Zababben dan majalisa mai wakiltar mazabar Chikun a
majalisar dokoki ta jihar Kaduna Madami Garba Madami ya
rasu.

Madami Garba dai ya rasu ne sakamakon wani rashin lafiyar da ba a bayyana ba a wani asibiti da ke garin Kaduna.

Duk da cewa zababben dan majalisar ya karbi takardar shaidar sake komawa kan kujerar sa daga hukumar zabe, amma bai samu damar halartar taron kaddamar da zauren majalisar ba a ranar 13 ga watan Yuni sakamakon rashin lafiyar.

Marigayi Madami ya taba rike mukamin shugaban karamar hukumar Chikun, kuma tsohon kwamishina a jihar Kaduna kafin ya tsaya takara, inda ya kada dan majalisa mai wakiltar mazabar Chikun a zaben majalisar dokoki ta jihar da aka gudanar a karkashin jam’iyyar PDP.

Leave a Reply