Kakakin Yaɗa Labarai na kwamitin yakin neman zaben Atiku
Abubakar Dino Melaye, ya bayyana a gaban Kotun Ɗaukaka
Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa a matsayin mai bada shaida.
Dino Melaye, wanda ya bayyana a matsayin mai bada shaida na musamman ga Atiku Abubakar, ya ce sakamakon ƙarshe na zaɓen shugaban ƙasa da INEC ta bayyana wa duniya ba daidai ta zuba su a komfuta ba.
Lauyan Atiku Abubakar Chris Uche ne ya gabatar da Dino Melaye, wanda ya shaida wa kotun cewa shi ne wakilin PDP a Cibiyar Tattara Sakamakon Zaɓe.
Ya ce ya ƙi yarda ya sa hannu a kan sakamakon zaɓen da hukumar zabe ta fitar, saboda ba a zuba su cikin komfuta kamar yadda ya dace ba.
Dino Melaye, ya ce ya fice daga Cibiyar Tattara Sakamakon Zaɓen ce tun kafin a kai ga bayyana sakamakon, bayan ya gano an yi kumbiya-kumbiya wajen zuba sakamakon zaɓen a komfuta don a kada Atiku Abubakar.














































