Home Home Za Mu Ba Da Shawarar Karin Albashi Don Taimaka Wa ‘Yan Kasa...

Za Mu Ba Da Shawarar Karin Albashi Don Taimaka Wa ‘Yan Kasa – Gwamna Bala

258
0

Gwamnan Jihar Bauchi Bala Muhammad, ya ce kwamitin da Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa  ta kafa, wanda aka dora wa alhakin bada shawarwarin hanyoyin da za a bi wajen raba wa ‘yan Nijeriya tallafi da gudunmawa sakamakon radadin cire tallafin Mai, za su gudanar da aikin su domin muradin ‘yan kasa baki daya.

Bala Muhammad, wanda ya ke wakiltar shiyyar Arewa Maso Gabas a cikin kwamitin, ya shaida hakan ne a lokacin da ya ke ganawa da ‘yan jarida a Bauchi.

Ya ce ‘yan kwamitin za su tabbatar da ganin duk ‘yan Nijeriya  sun samu tallafin a kowane bangare, domin rage radadin halin da aka tsinci kai sakamakon cire tallafin Mai ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba.

Gwamna Bala, ya ce duk Gwamnonin da ke bangaren adawa da na gwamnati mai ci, sun fahimci matakin da gwamnatin tarayya ta dauka bisa dacewa, don haka akwai tabbacin ba za a siyasantar da yunkurin ba.

Leave a Reply