Kwamitin kar-ta-kwana na yaki da safarar mutane, ya kama wani saurayi da budurwar sa bisa zargin saida jaririn da su ka haifa don su sayi miyagun kwayoyi.
An dai kama Anthony Igbinogun da budurwar sa Joy Umukoro da wata kawar su Precious James, wadda ake zargin ita yi uwa ta yi makarbiya wajen kulla haramtaccen cinikin ga wani matsafi a birnin Fatakwal na Jihar Rivers.
Da ta ke manema labarai jawabi a birnin Benin na Jihar Edo, Shugabar sashen bincike ta kwamitin Abigail Ihonre, ta ce an saida jaririn ne a kan Naira miliyan daya da dubu 700, kuma yanzu haka bincike ya yi nisa wajen ganin an kwato jaririn tare da kama wanda ya sayi jaririn dan wata daya.
Sai dai mahaifiyar jaririn ta ce, an saida jaririn ne a kan Naira dubu 700, inda aka ba su tsabar kudi Naira dubu 500, sai kuma wanda ya hada su da mai sayen aka ba shi naira dubu 170, yayin da ragowar kudin aka sayi kwayoyi da su.
A na shi bangaren, mahaifin jaririn ya amsa cewa, bayan budurwar shi ta ba shi shawarar a saida jaririn ya kuma amince ciniki ya fada, an ba shi naira dubu 100 ne kacal daga cikin kudin.














































