Home Labaru Za Ayi Gagarimin Rusau A Abuja

Za Ayi Gagarimin Rusau A Abuja

95
0

Shugaban hukumar Raya Birnin Tarayya Abuja Shehu
Ahmed, ya ce za su rusa duk gidajen da aka gina a kan hanyar
ruwa a birnin Abuja.

Shehu Ahmed ya sanar da haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, inda ya ce rusa gidajen ya zama dole saboda sun toshe hanyoyin ruwa, wanda hakan ya ke janyo ambaliya idan aka yi ruwa mai yawa.

Ya ce Gidajen da ke Trademark dai su na daga cikin gidajen da su ka yi wa shaida domin rusa su, kuma tun a shekarun da su ka gabata su ke sanar da mazaunan wurin halin da ake ciki na ambaliyar ruwa, amma su ka yi watsi da maganar su.

Shehu Ahmed, ya ce hukumar FCDA za ta rusa ofishin ‘yan sandan da ke Trademark, amma ta ware wa jami’an tsaron wuri domin ci-gaba da aikin su na samar da tsaro.

Leave a Reply