Home Labaru Kasuwanci Farashin Man Fetur Ya Faɗi A Defo-Defon Najeriya – IPMAN

Farashin Man Fetur Ya Faɗi A Defo-Defon Najeriya – IPMAN

375
0

Farashin man fetur ya karye a defo-defo na Nijeriya, a daidai
lokacin da ake raɗe-raɗin ƙarin farashin man zuwa naira 700 a
kan duk lita ɗaya.

Ƙungiyar dillalan man fetur ta Nijeriya, IPMAN ta tabbatar da karyewar farashin, inda ta ce ana saida shi a kan naira ɗari huɗu da ɗoriya, saɓanin sama da naira ɗari biyar a kan duk lita guda.

Shugaban ƙungiyar reshen arewacin Nijeriya Bashir Ahmed Danmalam, ya ce farashin ya karye ne saboda ƙarancin masusaye kuma za a samu rangwame har a gidajen mai.

Bashir Danmalam, ya ce tun kafin a tafi hutun sallah farashin man fetur ya fara sauka, kuma yanzu haka man fetur a defo- defo da ke Lagos da Warri da Calabar an samu sauƙi domin ana samun shi ƙasa da naira ɗari huɗu.

Leave a Reply