Home Labaru Zaɓen Anambra: Za A Yi Zaɓen ‘Inkonkulusib’ Ranar Talata – INEC

Zaɓen Anambra: Za A Yi Zaɓen ‘Inkonkulusib’ Ranar Talata – INEC

85
0

Hukumar Zaɓe mai zaman kan ta ta Ƙasa INEC, ta ce za a yi zaɓen da ta ce bai kammala ba a jihar Anambra ranar Talata, 9 Ga Nuwamba na shekara ta 2021.

Babbar Jami’ar Zaɓe Florence Obi, ta ce zaɓen ya zama wanda bai kammala ba, domin ba a samu damar yin zaɓe a Ƙaramar Hukumar Ihiala ba.

Ƙaramar Hukumar Ihiala dai ta na da waɗanda ke da rajista har sama da mutane dubu 148, kamar yadda Obi ta tabbatar wa manema labarai, inda ta ce ba a samu gudanar da zaɓe a yankin ba saboda matsalar kai kayan zaɓe da malaman zaɓe.

Yanzu haka dai Charles Soludo na jam’iyyar APGA ke kan gaba da ƙuri’u dubu 103 da 946, yayin da Valentine Ozigbo na jam’iyyar PDP ke bin shi da ƙuri’u dubu  51 da 323.